CBN ya musanta bidiyon jabun naira 2000 da 5000; da ya bayyana a shafukan sada zumunta.

Wani bidiyo dauke da bandiran naira 2000 da kuma 5000 sun sake bulla a shafukan shafukan sada zumunta, ko da yake dai an samu bullar farko na kudin ne a shekarar ta 2020.

Amma bayan da Babban Bankin Najeriya – CBN, ya bayyana cewar zai sauya wasu kudaden kasar, sai aka soma rarraba wannan bidiyon.

Babban bankin Najeriya – CBN a wani bidiyo mai tsawon dakika 30 da ya wallafa a ranar 31 ga watan Mayu ya musanta sahihancin wannan bidiyon.

Duk da gargadin da CBN ya yi, amma an ci gaba da rarraba bidiyon jabun kudin a shafukan sada zumunta .

Leave a Reply