Cacar-baki ta kaure tsakanin Rundunar ‘Yan Sandan a Najeriya da Hukumar Yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa dangane da kama kwamandan runduna ta musamman dake yaki da masu aikata laifuffuka, Abba Kyari wanda ake tuhuma da hannu wajen safarar miyagun kwayoyi.
Rahotanni sun bayyana cewa bayan kama Mukaddashin kwamishinan ‘Yan Sandan Abba Kyari tare da wasu jami’ansa, Rundunar ‘Yan Sandan ta zargi wasu daga cikin jami’an Hukumar ta NDLEA da hannu dumu dumu wajen aikata laifin.
Sai dai mai magana da yawun Hukumar sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa Femi Babafemi yayi watsi da zargin inda yake cewa ba zasu kare wani jami’in su da aka tabbatar da laifi akan sa ba, yayin da ake cigaba da gudanar da bincike akan lamarin bayan damke Abba Kyari.
Babafemi yayi nuni da jawaban Abba kyari da aka nada lokacin da yake tattaunawa da jami’in NDLEA tare da na ASP James Bawa lokacin da ake gudanar da bincike akan sa akan yadda masu safarar kwayar suka tuntube su.