Buhari ya tsawaita zamansa a Landan domin duba lafiyar haƙorinsa


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai tsawaita zamansa a London da mako guda, in ji kakakinsa Femi Adesina.

Wata sanarwa dauke da sa hannun Adesina ta ce likitan hakori da ke duba shugaban na Najeriya ne ya ba da shawara kan ya tsawaita zaman nasa a London domin a mai aiki.

Buhari na daga cikin shugabannin kasashen duniya da suka halarci bikin nadin sarautar Sarki Charles III da aka yi a London a ranar Asabar da ta gabata.

“Kwararren likitan ya bukaci ya ga Buhari cikin kwanaki biyar domin wani aiki da aka riga aka fara yi masa.” Sanarwar ta Adesina wacce VOA ta samu kwafi ta ce.

A ranar 29 ga wannan wata na Mayu, Buhari zai kammala wa’adin mulkinsa na biyu.

Zai mika shugabancin kasar ga Bola Ahmed Tinubu da ya lashe zaben da aka yi a watan Fabrairun da ya gabata.

Leave a Reply