Buhari ya taya Tinubu murnar lashe zaɓen shugaban Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari ya taya zaɓaɓɓen shugaban kasar Bola Tinubu murna, yana mai cewa shi ne mutumin da ya fi dacewa da aikin.

“Yanzu zan yi aiki tare da shi da tawagarsa don tabbatar da mika mulki cikin tsari,” in ji shugaban a wata sanarwa.

Jam’iyyun adawa sun yi ta cece-ku-ce kan nasarar da mista Tinubu ya samu, inda suka bukaci da a sake gudanar da zaɓen.

Wa’adin mulkin shugaba Buhari karo na biyu na ɗab da karewa.

Buhari ya ce duk da cewa an samu ‘yan kura-kurai a gudanar da zaɓen, amma ya ce ko shakka babu zaɓen ya kasance mai sahihi.

Ya ce duk wanda bai yadda da sakamakon zaɓen ba, zai iya zuwa kotu ba tayar da fitina ba.

Leave a Reply