‘Buhari ya sha yabo a wajen shugabannin Afirka a Nijar’

A yau ne ake buɗe taron shugabannin ƙasashen Afirka kan hanyar samar da masana’antu da faɗaɗa hanyoyin inganta tattalin arziƙi, a jamhuriyar Nijar.

Sai dai gabanin taron, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da wata hanya mai tsawon kilomita 3.8 a Yamai babban birnin ƙasar, wadda aka sanya wa sunansa.

Haka nan kuma an yi wani bukin na ƙaddamar da fassarar littafi a kan salon shugabancin Muhammadu Buhari, zuwa harshen Faransanci, wanda Farfesa John Paden na jami’ar Mason University da ke Virgina ta ƙasar Amurka ya wallafa.

Wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar ta hannun mai taimaka wa shugaban ƙasar kan yaɗa labaru, Garba Shehu, ta ce Shugaba Buhari ya sha yabo a bakunan shugabannin ƙasashen da suka yi jawabi.

Shugabannin da suka hadar da  Mohammed Bazoum na jamhoriyyar Nijar, Umaro Embaló na Kasar Guinea Bissau da tsohon shugaban kasar ta Nijar  Mahamadou Issoufou harma da shugaban rikon kwarya na kasar  Chadi  Mahamat Deby Itno.

Leave a Reply