Buhari ya amince da sayo motoci masu sulke 400 don kare Abuja da Nasarawa da Niger

Shugaban Najeriya Muhamadu Buhari ya amince da sayo motocin yaƙi masu sulki 400 ga dakarun soji, domin kare babban birnin ƙasar Abuja da jihar Nasarawa da wasu yankuna na jihar Niger.

Sabon babban kwamandan rundunar soji mai lura da yankin Manjo Janar Mohammed Usman,ne ya bayyana haka ranar Laraba a cikin jawabin godiya da ya gabatar jim kaɗan bayan shugaba Buhari ya yi masa ƙarin girma.

Manjo Janar Usman ya gode wa shugaban ƙasar saboda jajircewarsa da taimakon da ya ke bai wa rundunar, ciki har da amincewa da sayo motocin sulken 400, waɗanda ya ce sun isa wajen kare yankinsa da ya ƙunshi babban birnin ƙasar, da jihar Nasarawa da kuma wasu yankunan jihar Niger.

Haka kuma ya bayyana jin daɗinsa game da ƙarin girman da aka yi masa, yana mai cewa hakan zai taimaka masa wajen gudanar da aikinsa.

Leave a Reply