Buhari ya ƙi sanya hannu kan dokar da ta bai wa majalisa damar gayyatar shugaban ƙasa

Shugaban majalisar dattawan Najeriya Sanata Ahmad Lawan, ya ce majalisar za ta sake nazarin sauran dokoki 19 da majalisar ta gyara wa fuska, waɗanda kuma shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya ƙi sanya wa hannu.

Sanata Lawan ya bayyana haka a lokacin zaman majalisar na ranar Talata.

A cikin watan Janairun da ya gabata ne majalisar ta aike wa shugaba Buhari wasu dokoki 35 da majalisar ta yi wa gyaran fuska, domin amincewa da su.

To sai dai a makon da ya gabata shugaban ƙasar ya amince da dokoki 16 cikin 35 din da ta aike masa.

Sanata Lawan ya ce ɗaya daga cikin sabbin dokokin da shugaban ƙasar ya sanya wa hannu ita ce dokar da ta tanadi samar da ‘yancin gashin kai a ɓangaren kashe kuɗade ga majalisun dokokin jiha da ɓangaren shari’a.

To sai dai ɗaya daga cikin dokoki dokoki 19 da shugaban ƙasar ya ƙi sanya hannu a kai har da dokar da ta bai wa majalisar dokoki ta ƙasa da majalisun dokokin jihohi damar gayyatar shugaban ƙasa ko gwamna, domin yin bayani kan wasu abubuwan da majalisar dokoki ta ƙasa ko majalisun dokokin jihohi ke da damar aiwatarwa.

Da kuma dokar da aka yi wa gyaran fuska wadda ta tanadi tilasta wa shugaban ƙasa ko gwamna bin umarni ko yin biyayya ga gayyatar da majalisa ta yi masa.

Leave a Reply