Buhari ba zai halarci taron sauyin yanayi ba a Masar

Shugaban Muhammadu Buhari ba zai halarci taron COP27 ba kan sauyin yanayi da zai gudana a garin Sharm El Sheikh na ƙasar Masar.

A madadin haka, Buhari ya umarci Ministan Muhalli Mohammed Abdullahi ya wakilce shi a taron da zai gudana daga 6 zuwa 18 ga watan Disamban 2022.

Shugaban yana birnin Landan yanzu haka don a duba lafiyarsa bayan ya fita daga Najeriya ranar Litinin.

Ministan zai jagoranci tawagar Najeriya a ɓangarorin taro da kuma karanta jawabin ƙasar. Kazalika, zai halarci taruka game da shirin Najeriya na sauya alƙiblar makamashinta.

Sauran ministoci biyar da za su yi wa ministan rakiya su ne: Ministar Kuɗi Zainab Shamsuna, Ministan Lantarki Abubakar Aliyu, Ministar jinkai da agajin gaggawa Sadiya Farouq, Ministan Noma Mohammad Mahumud Abubakar da dai sauransu.

Leave a Reply