Buƙatar ‘Yan Ƙwadago Kan Mafi Ƙarancin Albashi ₦494,000 Duk Shekara Zai Kai Naira Tiriliyan 9.5 Kuma Abu ne Wanda Ba Zai Dore Ba

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya ce mafi ƙarancin albashi na ƙasa N494,000 da Ƙungiyar Ƙwadago (NLC) ke nema, wanda ya kai jimillar naira tiriliyan 9.5 a duk shekara, na iya gurgunta tattalin arzikin ƙasa da kuma kawo cikas ga jin daɗin ‘yan Nijeriya sama da miliyan 200.

Idris ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai a Abuja, yayin da yake mayar da martani ga barazanar da ƙungiyar ƙwadagon ta yi na tafiya yajin aiki idan har ba a biya musu buƙatunsu ba.
Ministan ya ce duk da cewa Ƙungiyar Ƙwadago ta damu da albashin ma’aikata kusan miliyan 1.2, Gwamnatin Tarayya ta damu da jin daɗin ‘yan Nijeriya sama da miliyan 200 bisa la’akari da ƙa’idojinta na araha, ɗorewa, da kuma lafiyar tattalin arzikin ƙasar baki ɗaya.
Ya ce saboda jajircewar da gwamnatin Tinubu ta yi wajen kyautata rayuwar ma’aikata, za a ci gaba da bayar da albashin ma’aikatan tarayya N35,000 har sai an ɓullo da sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa.

Leave a Reply