Birtaniya ta janye shirinta na mayar da ofishin jakadancinta na Isra’ila Birnin Kudus.

Gwamnatin Birtaniya ta tabbatar cewa ba ta da niyyar mayar da ofishin jakadancinta na Isra’ila daga Tel-Aviv zuwa Birnin Kudus.

Kakakin sabon Firaiminista Rishi Sunak, ne ya tabbatar da hakan a taron manema labarai.

A watan Satumba da ya wuce, tsohuwar Firaiminista Liz Truss, ta sanar da duba yiwuwar sauya mazaunin ofishin, lamarin da ya fusata Falasdinawa da suka ce hakan ya saba wa dokokin duniya.

Kuma hakan suka ce zai janyo karin tashin hankali a yankin wanda ya kasance ana fama da shi shekara da shekaru.

Isra’ila na kallon birnin Kudus a matsayin babban birninta, yayin da Falasdinawa ke ganin gabashin Kudus a matsayin nasu, inda Yahudawa ‘yan kama wuri zauna suka mallake, da kuma suke fatan ya kasance babban birninsu nan gaba.

Leave a Reply