Biden ya ce masu zaben rabin wa’adi na sake fito da matsalolin Amurkawa

Shugaba Biden ya ce masu zabe sun yi amfani da damarsu ta zaben rabin wa’adi na ‘yan majalisar dokokin Amurka da aka yi ranar Talata, inda suka bayyana damuwarsu da abubuwan da ke ci musu tuwo a kwarya.

Batutuwan sun shafi hauhawar farashi da tsadar rayuwa da tsaro da dimukuradiyya da kuma batun ‘yancin zub da ciki.

Da ya ke jawabi ga taron manema labarai ya ce ya ji dadin yadda sakamakon ya kasance zuwa yanzu.

Biden ya ce, yayin da ‘yan jarida da masu fashin baki ke hasashen samun wani gagarumin sauyi, to bai faru ba.

Shugaban ya ce duk da yadda sakamako ya karkata, har yanzu yawancin Amurkawa na goyon bayan manufa da tsare-tsarensa na tattalin arziki.

Leave a Reply