Ranar Asabar Real Madrid ta doke Celta Vigo da ci 2-1 a wasan mako na 30 a gasar La Liga da suka kara.
Celta ta ci kwallo ta hannun Nolito, yayin da Karim Benzema ya zura biyu a raga a wasan.
Hakan ne ya sa ya yi kan-kan-kan da tarihin da Alfredo Di Stefano ya kafa a matakin na uku a yawan cin kwallaye a Real Madrid a La Liga.
Benzema dan kasar Faransa ya zura kwallo 216 a Real Madrid, hakan na nufin yana biye da Raul, wanda keda 228 da kuma na daya Cristiano Ronaldo mai 312 a raga.
Kawo yanzu Benzema ya ci kwallo 34 a kakar bana a Real Madrid a dukkan fafatawa – wanda ya fara cin kwallo a kungiyar Santiago Bernabeu a mako na uku a kakar 2009/10 a wasa da Xerez.
Cikin kakar da ya yi a kungiyar Sifaniya ya lashe kofi 20 da suka hada da Champions Leagues hudu da Club World Cups hudu da European Super Cups uku da LaLigas uku da Copa del Rey biyu da Spanish Super Cups hudu.
Kawo yanzo Benzema yana da kwallo 24 a La Liga a bana, yayi kan-kan-kan da yawan cin kwallo da ya yi a kakar 2015/16.
Saura wasa takwas a karkare La Liga a bana, shine kan gaba a takarar lashe kyautar takalmin zinare da ake kira pichichi.
Karo na hudu kenan da Benzema ya ci kwallo fiye da 20 a kakar tamaula da ya hada da 2020/21 da ya ci 23 da kuma, 2019/20 da 2018/19 da 2011/12 da ya zura 21 a raga.