Benzema ya lashe kyautar Ballon d’Or a tarihin rayuwarsa

Dan wasan Real Madrid, Karim Benzema ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na duniya da ake kira Ballon d’Or.

Benzema ya ci kwallo 44 a wasa 46, wanda ya bayar da gudunmuwar da Real Madrid ta lashe La Liga da Champions League a 2021/22.

Lionel Messi mai rike da kyautar bara mai bakwai jumulla da Cristiano Ronaldo mai biyar, sun lashe 12 daga Ballon d’Or 13 baya.

‘Yar wasan Barcelona, Alexia Putellas ce ta sake lashe gwarzuwar kwallon kafa ta duniya ta 2022.

‘Yar kwallon Ingila da ta ci Euro 22 mai taka leda a Arsenal, Beth Mead ce ta biyu.

Manchester City, wadda take da ‘yan takara shida ta lashe kyautar kungiyar da ba kamarta.

An bayar da kyautar bana bisa kwazon dan wasa a kakar 2021/2022, maimakon shekara daya da ake yi a baya.

Benzema shi ne dan kasar Faransa na farko da ya lashe Ballon d’Or tun bayan 1998.

Zidane ne ya lashe kyautar 1998, kuma shi ne ya bai wa Benzema kyautar bana.

Jerin 20 din farko da suke kan gaba a taka leda a duniya a kyautar Ballon d’Or

1. Karim Benzema (Real Madrid, France).

2. Sadio Mane (Bayern Munich, Senegal).

3. Kevin de Bruyne (Manchester City, Belgium).

4. Robert Lewandowski (Barcelona, Poland).

5. Mohamed Salah (Liverpool, Egypt).

6. Kylian Mbappe (Paris St-Germain, France).

7. Thibaut Courtois (Real Madrid, Belgium).

8. Vinicius Junior (Real Madrid, Brazil).

9. Luka Modric (Real Madrid, Croatia).

10. Erling Haaland (Manchester City, Norway).

11. Son Heung-min (Tottenham Hotspur, South Korea)

12. Riyad Mahrez (Manchester City, Algeria).

13. Sebastien Haller (Borussia Dortmund, Ivory Coast).

14. Fabinho (Liverpool, Brazil) tied with Rafael Leao (AC Milan, Portugal).

16. Virgil van Dijk (Liverpool, Netherlands).

17. Luis Diaz (Liverpool, Colombia) tied with Dusan Vlahovic (Juventus, Serbia) and Casemiro (Manchester United, Brazil).

20. Cristiano Ronaldo (Manchester United, Portugal).

Leave a Reply