
A jadawalin da Fifa ta fitar tawagar Belgium ta ci gaba da rike matakinta na daya, inda Ingila take ta uku, bayan da Brazil ke ta biyu.
Wannan jadawalin ya hada da kwazon da kasashe suka yi a cikin watan Satumba a wasannin shiga kofin duniya da aka yi, wanda Belgium ta ci gaba da zama a kan mataki na daya.
Ingila ta hau kan Faransa mai rike da kofin duniya, yayin da Italiya wadda ta ci Ingila ta lashe Euro 2020 a wasan karshe a bana tana mataki na biyar da Argentina wadda ta lashe Copa America a bana ta shida a jerin jadawalin.
Portugal na saman makwabciyarta Sifaniya a matsayi na bakwai, Mexico ta ci gaba da zama ta tara, inda Denmark ta shiga cikin goman farko, bayan da Amurka ta yi kasa zuwa ta 13.
Iran ita ce jagaba a nahiyar Asia ta 22 a duniya, inda Senegal ce ta daya a nahiyar Afirka ta 20 a duniya sai Tunisia da Algeria da Moroco da Najeriya ta biyar ta 34 a duniya da kuma Masar ta shida kuma ta 48 a duniya, yayin da New Zealand ce ta daya a Oceania kuma ta 121.
Hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa za ta fitar da jadawalin kasashen da ke kan gaba a tamaula na gaba ranar 21 ga watan Oktoba.