Bayern na zawarcin Rice, Vinicius ba zai bar Real Madrid ba

Bayern Munich na ganin Declan Rice zai fi dacewa da ita, sai dai kuma tana da shaka kan miƙa tayinta ganin cewa Arsenal na kokarin saye ɗan wasan na Ingila mai shekara 24. (Sky Sport Germany)

Manchester United na tattaunawa da ɗan wasan Brazil da ke buga gaba, Neymar, mai shekara 31, da ke taka leda yanzu haka a Paris St-Germain. (L’Equipe – in French)

Man United na kokarin ganin ta cimma yarjejeniya da ɗan wasan Napoli Kim Min-jae, mai shekara 26, yayinda PSG ita ma ke nuna kwaɗayinta kan ɗan wasan asalin ƙasar Koriya ta Kudu. (Sun)

Barcelona na son dauko ɗan wasan tsakiya a Portugal Ruben Neves, mai shekara 26, daga Wolves a wannan kakar, sai dai hakan ya ta’alaka da tafiyar Ansu Fati mai shekara 20. (The Athletic – subscription required)

Idan Arsenal ta gaggara saye Rice, akwai ‘yan wasa irinsu Neves, da mai bugawa Real Socieded asalin Sifaniya, Martin Zubimendi da kuma ɗan wasan Brighton, Moises Caicedo a kan layi. (Mail)

Dan wasan Switzerland Granit Xhaka, mai shekara 30, ya ce kafin wasan karshe na kaka da Arsenal za ta buga zai tabbatar da makomarsa, yayinda kungiyar ta yi nisa a tattaunawa da ɗan wasan Beyer Leverkusen kan sama da £13m. (Standard)

AC Milan ta dage kan ganin ta dauko ɗan wasan Arsenal Folarin Balogun bayan burgeta da matashin mai shekara 21 ya yi a Reims, sai dai akwai kalubale da ta ke fuskanta daga RB Leipzig. (Calciomercato – in Italian)

Vinicius Jr ba shi da niyyar barin Real Madrid, duk da cewa ɗan wasan asalin Brazil mai shekara 22, na fuskantar kalaman kiyayya ko wariya daga magoya-bayan kungiyoyin hamayya.(90min)

Liverpool ta shiga jeren kungiyoyin da ke zawarcin ɗan wasan Ingila Marc Guehi mai shekara 22 daga Crystal Palace. (Mail)

Liverpool na kuma gab da cimma yarjejeniya da ɗan wasan Brighton mai shekara 24 asalin ƙasar Argentina Alexis Mac Allister. (Fabrizio Romano)

Manchester United ta shirya bai wa Anthony Martial damar barin kungiyar a wannan kaka. (Sun)

Bayern Munich ta fadawa Man United cewa dole su biya £22m domin cimma yarjejeniya kan ɗan wasanta Marcel Sabitzer, mai shekara 29. (Sky Sport Germany)

Nottingham Forest na son ganin ta cigaba da rike mai tsaron raga Keylor Navas, mai shekara 36, da ɗan wasan Brazil Renan Lodi, mai shekara 24. (90min)

Forest na kuma nuna zawarci kan ɗan wasan Italiya mai tsaron raga Michele di Gregorio, mai shekara 25. (Calciomercato – in Italian)

Leave a Reply