Barcelona ta bi sahun Liverpool da Manchester City da kuma Bayern Munich a fafutukar zawarcin dan gaba na gefe na Leeds kuma dan Brazil Raphinha, mai shekara 25, wanda kungiyarsa ta yi masa farashi fam miliyan 60. (Mirror)
Haka kuma Barcelona na sha’awar Robert Lewandowski, na Real Madrid kuma kyaftin din tawagar Poland mai shekara 33. (Sport – in Spanish)

Dan gaban Liverpool Divock Origi, mai shekara 26, na tattaunawa da abokan hamayya na gasar Italiya ta Serie A, AC Milan da Inter Milan a kan komawarsa daya daga cikinsu idan kwantiraginsa ya kare da Liverpool a bazara. (90min)
Manchester City na daga cikin kungiyoyin Premier da ke sa ido a kan dan wasan baya na gefe na Crystal Palace, Tyrick Mitchell bayan da dan bayan mai shekara 22 ya samu goron gayyata zuwa tawagar Ingila a karon farko.(Sun)