Barcelona ta sanar da tafka asarar Yuro miliyan 481 a kakar da ta wuce, kamar yadda ta fitar da hada-hadar kasuwancin 2020-21 ranar Laraba.
Kungiyar ta Caamp Nou ta ce ta tafka asarar, sakamakon bullar cutar korona da yin wasanni ba ‘yan kallo da ta kai ta rasa Yuro miliyan 181 da sauran kayayyakin da take sayarwa da suka yi kwantai.
Haka kuma samun kudin kungiyar ya yi kasa zuwa kasso 26 cikin 100 da ya kai Yuro miliyan 631, yayin da kashe kudin da take yi ya karu zuwa Yuro biliyan 1.16.
Shugaban Barcelona, Joan Laporta ya sanar wata biyu baya cewar bashin da ake bin kungiyar ya kai Yuro biliyan 1.35.
Hakan ne ya sa Lionel Messi ya bar kungiyar, bayan da Barcelona ba za ta iya biyan albashinsa ba, inda kyaftin din Argentina ya koma Paris St Germain da taka leda, haka kuma Antoine Griezman ya koma Atletico Madrid.
Darakta janar na Barcelona Ferran Revere ya fada ranar Laraba cewar tsohon shugaban kungiyar ne ya jefa su cikin wannan mawuyacin halin.
Ya kara da cewar ”sun sayo ‘yan wasan da ba za a samu ribarsu ba. Za a dauki kaka biyar nan gaba kafin kungiyar ta fara cin riba.”
Wannan halin kalubale da Barcelona ta shiga ya nuna koma baya da take fuskanta a wasanni, inda take ta tsakiyar teburin La Liga, sannan ta sha kasi a wasa biyu a Champions League a wasannin cikin rukuni a bana.