Barcelona na son maye gurbin Memphis Depay da Goncalo Guedes, Chelsea ta shirya rabuwa da Jorginho, Liverpool zatayi Gyara.

Barcelona na son maye gurbin Memphis Depay da Goncalo Guedes

Kungiyar ta Barcelona na son daukar dan wasan gaba na Wolverhampton Wanderers dake buga gasar firimiya ta kasar ingila, an rawaito cewa dai tuni dan wasa mai shekaru 26 sun tattauna da mai horas da babban kungiyar ta Barcelona Xavi Hernandez don jin shirye-shiryen kungiyar ta barca.

Barcelona dai tuni ta cimma yarjejeniya tsakaninta da Atletico Madrid kan kudi €3 million wajen cefenar da dan wasa Memphis Depay.

Chelsea ta shirya rabuwa da Jorginho

Jorginho Mai shekaru 31 ya kasance maid an wasa mai muhimmanci a shekarun da suka gabata, amma sabbin mamallaka kungiyar na son rage kasha kudade don haka zasu kyale dan wasa ya tafi a kyauta. Barcelona dai na daya daga cikin zaurawan da ke zawarcin jorginho sai kuma tsohuwar kungiyarsa ta SSC Napoli dake kasar italiya.

Bayern Munich ta dauki mai tsaron raga

Bayern Munich ta dauki mai tsaron raga daga Gladbach har zuwa karshen kakar wasan shekarar 2025.

Haka kuma kungiyar ta dauki dan wasa Konrad Laimer daga kuniyar RB Leipzig

Laimer mai shekaru 25 dai ba zai iso kungiyar ta Munich ba sai a watan July idan kwantaraginsa yakare tsakaninsa da RB Leipzig.

Liverpool na son musayar Naby Keita dan wasan Inter Milan Marcelo Brozovic

Brozovic dai ana alakan tashi da Barcelona amma Liverpool na son karawa Tsakiyar kungiyar armashi sakamkon rashin nasara da take ta faman yi a yan kwanakinnan.

Sannan an rawait cewa kuniyar na son Yanke alaka da dan wasa Arthur Melo da ta aroshi daga Juventus.

Leave a Reply