Barcelona na fuskantar tuhumar bayar da cin hanci ga alƙalan wasa

Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona na fuskantar tuhume-tuhume kan biyan wasu kuɗi da ƙungiyar ta yi wa Jose Maria Enriquez Negreira tsohon mataimakin shugaban kwamitin alƙalan wasa.

A watan da ya gabata aka gano cewa ƙungiyar ta biya euro miliyan 8.m ga Negreira tare da wani kamfani da ya mallaka tsakanin shekarar 2001 zuwa 2018.

An faɗa wa wata kotu a birnin Barcelona ranar Juma’a cewa ana tuhumar tsoffin jami’an ƙungiyar tare da Negreira da aikata laifin ”cin hanci” da ”cin amana” da ƙarya a nasarorin ƙungiyar”

Ofishin babban mai shigar da ƙara na birnin Barcelona na zargin ƙungiyar tare da tsoffin shugabanninta Josep Maria Bartomeu da Sandro Rosell da hannu a aikata laifukan.

“Ƙungiyar Barcelona ta ƙulla yarjejeniyar baka da Jose Maria Enriquez Negreira a matsayinsa na mataimakin shugaban kwamitin alƙalan wasa, inda ta riƙa ba shi kuɗi domin ɗaukar matakan da za su riƙa taimaka wa ƙungiyar a hukuncin da alƙalan wasa za su riƙa yankewa a lokacin da ƙungiyar ke wasa” kamar yadda ofishin babban mai shigar da ƙarar ya bayyana.

A watan da ya gabata shugaban gasar La Liga Javier Tebas ya ce dole shugaban ƙungiyar Barcelona na yanzu Joan Laporta ya sauka daga muƙaminsa matuƙar ya kasa yin bayani game da biyan kuɗaɗen da ake zargin ƙungiyar da aikatawa.

Laporta ya mayar da martani da cewa ”ko da ya sauka daga muƙaminsa mista Tebas ba zai samu abinda yake so ba”.

Tuhumar na zuwa ne kwana uku bayan da Laporta ya kafe cewa ƙungiyarsa ba ta taɓa sayen alƙalin wasa ba.

“Bari na gaya muku gaskiyar magana Barca ba ta taɓa sayen alƙalan wasa ba, kuma ba ta da niyyar sayen alƙalan wasa, ba za ta taɓa ba”, kamar yadda shugaban ƙungiyar ya bayyana ranara Talata.

Leave a Reply