Bankin Raya Afrika Zai Bai Wa Najeriya Tallafin Dala Milyan 134 Don Bunkasa Noma

Bankin raya kasashen nahiyar Afrika ya sha alwashin tallafa wa bangaren noma a Najeriya da jarin dala milyan 134 da nufin bunkasa noman kayan abinci.

Shugaban bankin, Akinwunmi Adesina ne ya bayyana wannan kuduri yayin ziyarar Cibiyar Nazarin Noman Tsandauri ta Jami’ar Bayero da ke Kano.

Adesina, ya kuma jaddada muhimmancin samar wa manoma bayanai a kan noman zamani musamman ma yanzu da ake fama da kalubalen sauyin yanayi.

Ya jinjinawa kokarin shugaban Jami’ar Bayero ta Kano, Farfesa Sagir Adamu Abbas da daraktan cibiyar nazarin noman tsandauri, Jibrin Muhammad Jibrin saboda tallafin da suke bai wa manoma wajen yin amfani da fasaha a harkar noma a irin wannan lokaci da ake yaki da sauyin yanayi.

Leave a Reply