Bamu ceto jami’ar sojin da aka sace ‘yan IPOB suka sace ba — Sojin Najeriya

Hedikwatar tsaron Najeriya ta  musanta rahotanin da ke cewa sojojin ƙasar sun kuɓutar da wata jami’ar soja,  da ‘ƴan bindiga suka yi garkuwa da ita a jihar Imo da ke kudancin kasar.

A farkon makon da ya gabata ne mutanen da ba a san ko su wane ne ba suka sace matar, inda suka yi mata bidiyo tare da yaɗawa a shafukan sada zumunta.

Sanarwar da hedikwatar tsaron ta fitar ta ce sojoji za su ci gaba da ƙoƙarin kuɓutar da ita tare da hukunta waɗanda suka  yi garkuwa da ita.

Hedikwatar ta ce rahotanin da suka karaɗe shafukan sada zumunta na kuɓutar da laftanal P.P Johnson ba gaskiya ba ne, sai dai rundunarsu na ci gaba da ƙoƙari domin kuɓutar da itan.Ta ce hoton bidiyo da ake yaɗawa da ke nuna wani farmaki da jami’anta suka kai, ba sabo ba ne.

Leave a Reply