Babu wanda zai kada kuri’a sai ya na da PVC – INEC

Anan ma dai Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC ta jaddada cewa babu wanda za a bari ya jefa kuri’a a babban zaben kasar nan mai zuwa sai ya nuna katin zabe na dindindin.

Shugaban hukumar na kasa Farfesa Mahmud Yakubu ne ya bayyana haka a lokacin kaddamar da taron sabbin kwamishinonin zabe na hukumar, wanda aka yi a jihar Legas.

Mahmud ya bukaci al’ummar kasar nan da su yi watsi da jita-jitar da ke cewa mutum na iya kada kuri’a a ranar zabe ba tare da katin zaben na PVC ba.

Ya ce sashe na 47(1) na dokar zabe ta 2022 ta ce duk wanda zai kada kuri’a zai gabatar da katin zabensa ga jami’in zabe domin tantancewa a runfar zaben da ya yi rajista.

Saboda haka ya ce dokar ba ta sauya ba, wajibi bine duk wanda zai kada kuri’a ya gabatar da katin zaben sa ga jami’an zabe.

Leave a Reply