Babban sufeton ‘yan sandan Najeriya ya roki Kotu ta soke kai shi kurkuku

Babban sufeton ’Yan Sandan Najeriya, Usman Baba Alkali, ya bukaci kotu da ta soke hukuncin daure shi da aka yi a gidan yari na tsawon watanni uku.

Shugaban ’yan sandan na neman haka ne a gaban Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja, bayan da wata kotu ta sa a daure shi na watanni uku a gidan yari kan raina umarninta na dawo da Patrick C. Okoli bakin aikinsa na dan sanda, saboda sallamar sa ba bisa ka’ida ba.

Kakakin ’Yan Sandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi, cikin sanarwa da ya fitar a wannan Jumma’a ya ce Shugaban yan sandan ya bayyana cewa ba a nada shi mukamin ba a lokacin da aka fara shari’ar kuma aka amince da sake dawo da Patrick C. Okoli bakin aikinsa, hakan ya faru ne a lokacin magabacinsa.

Bukatar da Sufeto-Janar din ya shigar ta bayyana cewa tun kafin umarnin kotun da ta bayar a watan Nuwamban 2018 da Janairu 2019, magabacinsa ya aike wa Hukumar Kula da Harkokin Aikin Dan Sanda, takardar neman ta bai wa Okoli takardar dawo da shi bakin aiki da kuma kara masa girma zuwa matakin da ya dace.

Leave a Reply