Babban jami’in diflomasiyyar China na ziyara a Moscow

Babban jami’in diflomasiyyar China, Wang Yi, ya je birnin Moscow na Rasha domin tattauna da abokan huldarsu.

Mista Wang ya faɗawa Sakataren kwamitin tsaron Rasha, Nikolai Patrushev, cewa alaka tsakanin kasashensu biyu na nan daram kamar karfin dutse.

Ya ce bangarorin biyu sun tattauna yada za su tunkari duk wani salon nuna musu cin zali ko tsangwama.

A ranar Asabar, Sakatare tsaro na Nato, Yens Stoltenberg, ya sake jadada damuwar da Amurka ke nunuwa kan yiwuwar China ta taimakawa Rasha da makaman yakar Ukraine.

A cikin wannan makon ne ake sa ran shugaba Xi Jinping zai fito ya yi jawabi kan neman sasanta rikicin Ukraine a siyasance.

Leave a Reply