Babban Bankin Najeriya ya bukaci yan  Kasar dasu  kara hakuri nan ba da jimawa ba komai zai daidaita

Gwamnan Babban Bankin Najeriya Dr. Olayemi Cardoso ya roki ‘yan kasar da su kara hakuri, saboda a cewar sa bankin na iya bakin kokarinsa wajen ganin ya dawo da darajar kudin kasar, wanda shi ne ya haifar da tsadar rayuwa da kasar ke fama da shi.

Mista Cardoso ya bayyana hakan ne yayin wani taro da ya gudana a Jami’ar Tarayya ta Ibadan, wanda ya samu wakilcin daya daga cikin jami’an bankin Dr. Usman Opanachi.

Gwamnan Babban Bankin ya kuma bayyana cewa duk lokacin da darajar Naira ta shiga wani hali, bankin shima ya na shiga mawuyacin yanayi, saboda haka, ana aiki tukuru a kai domin ganin cewa komai ya daidaita.

Leave a Reply