Babban Bankin Najeriya CBN Ya Soke Karbar Harajin Tura Kudi Ta Intanet

Babban Bankin Najeriya CBN ya soke sabon harajin tura kudi ta intanet da ya bullo da shi a kwanakin baya.

A kwanakin baya ne CBN ya ɓullo da sabon harajin mai suna Harajin Tsaron Intanet, na kashi 0.5% kan duk kudin da aka tura ta intanet.
Sanarwar CBN ya fitar sanar da bankunan kasuwanci da sauran cibiyoyin haɗar kudaden cewa,ya janye umarnin ya bayar na farko kan cirar harajin 0.5% na tsaron intanet daga masu tura kudi ta intanet.
Idan za’a iya tunawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci CBN ya soke harajin, wanda majalirsun ta kasa suka kira abun da rashin tausaya wa ’yan Najeriya.
Majalisar ta bayyana cewa babban bankin bai fahimci sashen dokar da ya yi amfani da shi wajen ɓullo da sabon harajin.

Leave a Reply