Allah Ya yi wa babban alkalin kotun ɗaukaka ƙara shiyar Kano Mai Shari’a Husseini Mukhtar rasuwa.
Mai Shari’a Husseini Mukhtar ya rasu ne a ranar Asabar a Abuja bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.
Ya rasu yana da shekara 67 a duniya.
Idan an jima za a yi jana’izarsa.