Ba Zai Yiwu Mu Sa Jami’ai Su Tsare Kowane Sashe Na Kan Iyakar Najeriya Ba -Aregbesola

Aregbesola yayin ganawa da manema labarai, ya ce ba zai yiwu a tura jami’ai ko ina su rika kula da tsaron kan iyakokin ba. Ya ce Najeriya na daga kasashe uku mafiya fadin kasa a Afirka, don haka ba zai yiwu a ce kowane inci na kan iyakarta za a iya girke jami’an tsaro don kula da shi ba. Wannan dalili, inji Aregbesola, ya sa kasar ta ke gab da rattaba hannu kan wata yarjejeniya da wani kamfanin kasar Sin don samar da na’urorin tauraron dan-adam da za su rika zuba ido kan iyakokin dare da rana.

Ministan ya kara da cewa akwai wani kalubale da ya shafi kan iyakokin na raba jama’a masu al’ada iri daya ya zama wannan gefe ya na wannan kasa wannan gefe kuma ya na waccar kasar.

Don tabbatar da wannan bayani, Ministan ya ce ya ce gidan wani Sarkin Yarbawa wato Kabiyesi a jihar Ogun ya samu layin kan iyaka ya raba gidan Sarkin a tsakanin Najeriya da ketare. Aregbesola ya ce don rage wannan kalubale ya zama da muhimmanci gwamnati ta jawo jama’a su hada kai.

Da ya ke magana kan batun kula da kan iyaka don samar da zaman lafiya na cikin gida, shugaban kungiyar manoma masara ta Najeriya Modibbo Sadeeq Ahmad Nafada ya ce ya dace a duba batun hanyoyin burtali da makiyaya ke bi zuwa sassan cikin kasa da ketare don sake raya su.

Modibbo Nafada ya ce cin kan iyakar burtali ya haddasa fitina tsakanin manoma da makiyaya wanda hakan ya yi zagon kasa ga tsaro , tattalin arzikin da kuma batun samar da abinci a Najeriya.

Jami’an kwastam da na shige da fice na bayyana cewa su na zuba ido kan hajoji da mutane da kan ratsa iyaka duk da hakan ba ya hana miyagun irin samun makamai ta hanyoyin dazukan iyakar.

Leave a Reply