Tsohon gwamnan jihar Jigawa, kuma jigo a jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya Sule Lamido, ya ce ba za ta yiwu, a mika wa yankin kudancin kasar takarar shugaban kasa a jam’iyyar a kakar zaben 2023 saboda kawai son kai ba.
Yayin wata hira da BBC Hausa, tsohon gwamnan ya ce ba laifi bane idan an yi hakan saboda tunanin zaman lafiya da kuma son farfado da tasirin jam’iyyar a yankin arewa, wadda ake sa ran za ta karbi mukamin shugabancin jam’iyyar.
”Idan ma haka ta tabbata, sai dai a yi saboda zaman lafiya, misali akwai wadanda ke cewa yanzu PDP ba ta da karsashi a yankin arewa, don haka akwai bukatar a samu wani daga yankin da aka tabbatar da sahihancinsa a bashi shugabancin don farfado da tasirinta, to idan an yi haka ba lafi bane, amma idan aka ce dole sai dai a kai kudu, to wannan ba za ta yiwu ba” inji shi.
Ya kara da cewa ”ai an taba yin haka a PDP, aka dauko Obasanjo aka ce shi kadai zai yi takara, amma ka ga ai ba dole aka yi wa mutane ba, an yi ne domin ci gaban kasa da kuma son tabbatar da zaman lafiya da karuwar arziki”
Da alama tsuguni bata kare ba kan matsayar da kwamtin gwamnan Enugu ifeanyi Ugwuanyi da babbar jam’iyyar hamayya a Najeriya PDP, da ya mika shugabancin jam’iyyar zuwa arewacin kasar.
Wasu daga cikin kusoshin jam’iyyar na kalubalantar matakin inda suke ganin an shirya wa yankin makarkashiya ne don mayar da takarar shugabancin kasar ga yankin kudu a shekarar 2023.
A wani taron da gwamnonin kudancin Najeriya suka gudanar a watan Yuli, sun ce dole shugabancin Najeriya ya kasance na karɓa-karɓa daga yankin arewaci zuwa kudanci, kuma suna son shugaban ƙasa da za a zaɓa a 2023 ya fito daga yankin kudancin ƙasar saboda abin da gwamnonin suka kira tabbatar da adalci.
Wannan batu ya janyo zazzafar muhawara a fadin kasar, inda kungiyar dattawan arewacin kasar ta ce babu wanda zai tilasta wa al`ummar yankinta zaɓen wani dan takarar shugaban kasa da ya fito daga kudancin ƙasar a zaben 2023.
Kakakin kungiyar dattawan na arewa Dr Hakeem Baba Ahmed ya shaida wa manema labarai cewa arewa tana da yawan masu zabe, don haka “yankin ba ya shakkar ko wace irin barazana.”