Ba Za A Yi Gagarumin Bikin Cikar Gwamnatin Tinubu Shekara Ɗaya Ba, In ji Ministan Yaɗa Labarai

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai Alhaji Mohammed Idris, ya ce ba za a yi wani gagarumin biki a ranar cikar gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu shekera ɗaya ba, sai dai ma ministoci da zasu gabatar da bayanai kan ma’aikatun su.

Idris ya bayyana haka ne a taron manema labarai na ministoci a ranar a Abuja, inda yace matakin ya yi daidai da muradin Tinubu na yi wa ƙasa hidima, da kuma amfani da albarkatun ƙasa yadda ya kamata domin amfanin ɗaukacin ‘yan Nijeriya.
Ministan ya buƙaci masu aikin yaɗa labarai da su yi aikin su da sanin ya-kamata tare da kishin ƙasa.
Ya nanata cewa, a wani ɓangare na bikin ranar, ministocin daban-daban za su fara gabatar da jawabai kan ayyukan ma’aikatun su domin sanin halin da kowace ma’aikata ke ciki.

Leave a Reply