Ba za a iya kutse a na’urar tattara sakamakon zabe ba – INEC

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC ta kara tabbatar wa ‘yan kasar nan cewa ba za a iya yin kutse domin sauya bayanan da ke cikin na’urorin tattara sakamakon zabe ba.

Babban mataimakin shugaban hukumar mai lura da sashen fasahar zamani Lawrence Bayode ne ya tabbatar da hakan a lokacin da yake amsa tambayoyi a wani shirin gidan Talbijin din a kasar nan, yana mai cewa ba za a iya yi wa na’urar kutse a ranar zabe ba. Ya kara da cewa hukumar zaben ta tsaurara matakai domin tabbatar da cewa ba a yi kutse a na’urorin ba.

Leave a Reply