Ba ma tsoron fuskantar kowacce kungiya – Rudiger

Antonio Rudiger ya ce suna da ƙwarin gwiwar samun nasara a kan Manchester City a wasan zagaye na biyu a Gasar Zakarun Turai da za su fafata a ranar Laraba.

Rudiger dan kwallon tawagar Jamus ya hana Erling Haaland sakat a karawar zagayen farko da suka yi a Santiago Bernabeu.

Ranar Talata 9 ga watan Mayu kungiyoyin suka tashi 1-1 a fafatawar ta hamayya.

“Duk da cewa City na da zaƙaƙuran ƴan wasa, amma mun yi nasarar taka musu burki a wasan farko, kuma mun san za su riƙe kwallo yadda ya kamata,” in ji Rudiger.

Tsohon ɗan wasan na Chelsea ya ce yana da ƙwarin gwiwar cewa za su samu nasara a wasan na ranar Laraba.

Real Madrid ce mai rike da Champions League na bara mai 14 jimilla.

Pep Guardiola ya lashe babban kofin zakarun Turai biyu a Barcelona, amma ya kasa ɗauka a kungiyar Etihad.

Leave a Reply