Australiya ta ƙaƙaba wa Iran takunkumi kan taimaka wa Rasha

Gwamnatin Australiya ta saka takunkumai kan wasu Iraniyawa uku da kuma kamfani ɗaya na ƙasar ta Iran kan zarginsu da samar da jirage marasa matuƙa ga Rasha.

Haka kuma, Ministan Harkokin Waje na Australiya Penny Wong ya lissafa jerin matakan da ƙasar za ta ɗauka kan jami’an Hisbah na Iran ɗin da kuma wasu mutum shida waɗanda ke da hannu wajen amfani da karfi don murƙushe masu zanga-zanga.

Kazalika, akwai wasu Rashawa bakwai waɗanda ƙasar ta saka wa takunkumi da ake zargi suna da hannu a yunƙurin da aka yi na kashe shugaban ƴan adawa na ƙasar Alexie Navalny.

Leave a Reply