Atletico na son daukar Memphis Depay Bayern Munich Na neman Mai tsaron raga.

Kungiyar kwallon kafa ta Atletico madrid ta nuna sha’awar daukar dan wasan gaba na Barcelona Memphis Depay don maye gurbin Felix da ya koma Chelsea a satin da ya gabata.
Depay mai shekaru 28, da kwantaraginsa zai kare a karshen kakar wasan damuke ciki, baya samun damar buga wasanni inda ya buga wasa hudu kacal
a dukkan gasuka a wannan kakar wasanni, sannan kuma ya koma dumama benci kasancewar dan wasa Lewandowsky.

Sahihan Rahotanni dai sun bayyana cewa Atletico ta samu kyakkyawan martani daga dan wasan, kuma da alamu barcelona a shirye take da
ta sayar da dan wasan.

Kungiyar ta Bayern Munich na da aiki Ja, wajen nemo karin mai tsaron gida inji mai horaswa Julian Nagelsmann.
Jamusawan dai na cikin mawuyacin hali sakamakon rauni da babban mai tsaron ragar su Manuel Neuer ya samu yayin atisaye,

Kasuwar yan wasanni ta rikici musamman ta bangaren mai tsaron raga, sakamakon yadda kungiyoyi dayawa na nema a irin gurbin

cewar Julian Nagelsmann.

yanzu haka dai Munich na da mai tsaron gida dake zaman ko ta kwana mai shekaru 19 da mai horar da kungiyar ke ganin bashi da gogewar
da zai rike ragar bayern munich.

Dan wasan tsakiya na AC Milan Bennacer ya sake sabunta kwantaraginsa a kungiyar.
Ismael Bennacer dai ya shiga kungiyar ta AC Milan daga kungiyar Empoli a shekarar 2019 inda ya buga was 129, sannan kuma ya jagoranci kungiyar ta
AC Milan a dukkuan wasanni 24 ta ta buga wannan kakar wasanni.

Leave a Reply