Atletico Madrid ta karbi bakuncin Barcelona, domin buga wasan mako na takwas a gasar La Liga ranar Asabar.
Bayan da Barcelona ta sha kashi a Champions League a gidan Benfica da ci 3-0 ranar Laraba, za ta fuskanci wani kalubalen a La Liga a gidan mai rike da kofin bara.
Atletico tana ta hudu a kan teburin gasar bana da maki 14, Barcelona kuwa tana ta bakwai da maki 12.
Kungiyoyin sun kara a bara a La Liga, inda Atletico ta yi nasara da ci 1-0 ranar 21 ga watan Nuwambar 2020, a wasa na biyu suka tashi 0-0 ranar 8 ga watan Mayun 2021 a Nou Camp.
Barcelona za ta fuskanci tsoffin ‘yan wasanta biyu da ke buga wa Atletico kwallo, wato Luis Suarez da ta sayar da shi a bara da Antoine Griezmann da yake buga wasannin aro a bana.