AS Roma na son daukar Ziyech, Arsenal Manchester United da Chelsea na Zawarcin Declan Rice
Akwai yiwuwar dan wasan tsakiyar West Ham Declan Rice, zai iya zuwa Arsenal a karshen kaka, duk da Chelsea da Manchester United za su shiga sahun masu neman dan wasan na Ingila. (Guardian)
Shugabannin kungiyar kwallon kafa ta Everton sun tattauna kan makomar kocin kungiyar Frank Lampard, har ma da batun wanda zai maye gurbin tsohon dan wasan tsakiyar na Ingila. (Telegraph)
Kocin Tottenham Antonio Conte, ya ce bai shirya yanke hukunci kan ci gaba da zama a kungiyar ba a yanzu, duk da gabatar masa da bukatar ya ci gaba da zama a White Hart Lane. (Sky Sports)

Roma ta tuntubi wakilin dan wasan gefen Chelsea da Maroko Hakim Ziyech, wanda suke tunanin saye da zarar suka sayar da dan wasan gabansu Zaniolo. (Sky Sports)
A wata mai kama da haka Everton ta shiga jerin masu neman Ziyech, yayin da take fadi tashin ganin bata kare a ukun karshe ba. (Mail)
Manchester United ta bi sahun PSG, wurin takarar sayen dan wasan Athletico Paranaense da Brazil, Vitor Roque. (Gazerre dello Sport)
Nottingham Forest na duba yiwuwar kawo golan PSG Keylor Navas, duk da tana fuskantar hamayya daga Bounemouth da Leicester kan dan kasar Costa Rica din. (Mundo Deportivo)
Kazalika Nothingham Forest din da Leicester har ma da Everton, na neman dan wasan gefen Brazil da Shakhtar Donetsk Tete, wanda yanzu haka ke zaman aro a Lyon. (Mail)

Barcelona ta ce tana jin dadin wasa da mai tsaron bayan Sifaniya Marcos Alonso, kuma tana duba yiwuwar tsawaita zamansa idan an kulle kasuwar watan Janairu. (Sport)
A Italiya kuwa Inter Milan na son dauko mai tsaron bayan Ingila Chris Smalling daga Roma kyauta. (Gazette dello Sport)