Tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha, ya ce idan ba a bar yankin kudu ya samar da shugaban kasa a 2023 ba, jam’iyyar APC za ta zama jam’iyyar siyasa ta arewa.
Ya kuma kalubalanci yankin kudu maso gabas da su gabatar da kwakkwaran dalilin da zai sa a amince dan kabilar Igbo ya zama shugaban kasa na gaba.
Jaridar Daily Trust ta rawaito shi yana faɗar hakan a wani taro mai taken “Tattaunawa da Owelle Rochas Okorocha a bikin cikarsa shekaru 59 ’, wanda ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya, reshen babban birnin kasa Abuja ta shirya.
“Ina goyon bayan gwamnonin kudu kan batun mayar da kujerar shugaban kasa yankin Kudu., mun fara da Kudu maso Yamma lokacin Shugaba Olusegun Obasanjo, ya zama shugaban kasa. Sannan mun koma Arewa lokacin muna da Yar’Adua. Kudanci kuma tare da Goodluck Jonathan, kuma yanzu Arewa ce ke da shugaba mai ci” inji shi.
“Don haka, me yasa za a canza wannan tsarin yayin da ya kamata mulki ya koma kudu? Abu ne mai kyau a ci gaba da tafiya yadda ake yi.
Idan ba a yi hakan ba, to APC ta zama jam’iyyar arewa, “in ji shi.