Ana ce-ce-ku-ce kan kirkiro ofishin ‘babbar ‘yar shugaban kasa’ a Kenya

‘Yan kasar Kenya da ke amfani da shafukan sada zumunta sun bayyana kaduwarsu bayan da suka fahimci cewa an kirkiro ofishin ‘yar shugaban kasa William Ruto.

A wani bidiyo da ya karade shafukan intanet, an ga ‘yar shugaban kasar ta biyu, Charlene Ruto tana yin jawabi a wurin wani taro a Tanzania inda ta gabatar da “tawagarta daga Kenya” ciki har da mai ba ta shawara da kuma wani wanda shi ne “shugaban cinikayya da zuba jari a ofishin ‘yar shugaban kasa”.

Mahalarta taron sun yi shewa da tafi lokacin da ta bayyana tawagar tata.

“Ban san abin da ya ba ku dariya ba,” a cewar Ms Ruto a yayin da take mayar da martani kuma take kokarin ci gaba da gabatar da tawagarta.A dokokin Kenya babu ofishin ‘yar shugaban kasa kuma ba a fitar da wata sanarwa ta kirkiro ofishin ba.

Leave a Reply