An Zabi Tsohon Shugaban Hukumar INEC Cikin Masu Sanya Idanu A Zaben Kasar Bangladesh

An zabi tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC Farfesa Attahiru Jega, da wasu sanannun masana guda 9 daga kungiyar kasashe rainon Ingila a matsayin wadanda zasu je kasar Bangladesh, domin sanya ido kan zaben kasar da zai gudana a ranar 7 ga watan Janairun shekarar 2024.

Babbar sakatariyar kungiyar kasashe rainon Ingila Rt. Hon. Patricia Scotland da ta bayyana hakan, tace matakin ya biyo bayan samun gayyata daga hukumar zabe ta kasar Bangladesh din domin sanya ido da kuma tabbatar da an gudanar da zaben bisa tsari.

Ta kuma sanar da cewa tsohon firaministan kasar Jamaica Hon. Bruce Golding shi ne zai jagoranci tawagar masu sanya idanun.

Tawagar dai za ta yi aiki da masu ruwa da tsaki da suka hadar da kungiyoyin fararen hula, Jami’iyyun siyasa, jami’an ‘yansanda da ma ‘yan jarida wajen ganin anyi abin da ya dace yayin gabatar da zaben.

Leave a Reply