An yi sabuwar dokar haramta wa likitoci yajin aiki a Zimbabwe

An haramta wa ma’aikatan lafiya a Zimbabwe shiga yajin aikin da ya zarta sa’o’i 72, inda waɗanda suka saɓa dokar za su iya fuskantar hukuncin ɗaurin wata shida, kamar yadda sabuwar dokar ta nuna.

Ƙungiyar likitocin ƙasar da kuma ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam sun ce sabuwar dokar za ta ƙara ‘dagula’ al’amura a ƙasar, tare da tilasta wa likitocin neman aiki a ƙasashen waje.

Likitoci da ma’aikatan jinya a ƙasar dai sun sha shiga yajin aiki kan matsalar albashi da ƙarancin kayan aiki da magunguna.

Kusan ma’aikatan lafiya 4,000 ne aka ƙiyasta cewa sun ajiye aiki a ƙasar ake kuma zargin sun nemi aiki a ƙasashen ƙetare a shekarar da ta gabata.

Leave a Reply