AN yanke wa hamshakin attajirin Hong Kong, Jimmy Lai hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru biyar da watanni tara.

Jimmy Lai wanda ya kafa jaridar Apple Daily, wata jarida mai sukar ikon kasar China da aka tilastawa rufewa,ya shafe watanni ashirin a gidan yari a baya-bayan nan saboda halartar zanga-zanga da tarukan da ba a yarda da su ba.

Jimmy Lai na da shekaru 75, har yanzu za a yi masa shari’a nan ba da jimawa ba saboda  hadin gwiwa da sojojin kasashen waje, wanda ya saba wa dokar tsaron kasa da China ta kafa wanda ke da hukuncin daurin rai da rai.

Yayin da zaman da ya yi a baya a gidan yari na da nasaba da rawar da ya taka a zanga-zangar neman dimokradiyyar shekara 2019.

Jimmy Lai da Wong Wai-keung, tsohon jami’in Apple Daily, an same su da laifin zamba a watan Oktoba.

A nasu bangaren, lauyoyin  sun ce ya kamata a ce shari’ar ta kasance batun farar hula ne maimakon shari’ar laifuka, inda suka kara da cewa yankin da abin ya shafa ya yi kadan.

Mista Wong, mai shekaru 61, an yanke masa hukuncin daurin watanni 21 a gidan yari.

Alkalin ya soki jaridar Apple Daily da laifin cin mutuncin a matsayinsa na sanannen kafafen yada labarai don mayar da ita garkuwar kariya, wanda ya hana mai shi yin aiki idan aka saba ka’idojin yarjejeniyar.

Leave a Reply