An Warware Shari’u Sama Da Dubu Saba’in Da Daya A Jihar Kano Cikin Shekarar 2023

Babbar alkaliyar jihar Kano, mai shari’a Dije Aboki ta bayyana cewa babbar kotun Kano ta warware shari’u a kalla 71,914 daga cikin 102,234 da aka samu a cikin shekarar 2023 da muka yi bankwana da ita.

Dije Aboki ta bayyana hakan ne yayin wani taro na musamman da aka shirya saboda alkalai da suka yi ritaya daga aiki, da kuma wadanda suka rasu a jihar Kano.

A yanzu haka dai Dije ta ce akwai shari’u guda 30,320 daga babbar kotun jiha, kotun majistire da kuma ta shari’a da suke kasa suna jiran a waiwaye su, kuma sun hada da na aikata laifuka da kuma tsakanin daidaikun mutane.

Kazalika ta yabawa wa gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf, bisa kammala gyaran kotun da ke kan titin Zaria, a yunkurin rage yawan shari’un da ake da su.

A nashi bangaren, Gwamna Abba Kabir ya jaddada goyon bayan gwamnatin sa ga fannin na shari’a domin tabbatar da adalci, da ma kyautata rayuwar ma’aikatan shari’a a jihar Kano.

Leave a Reply