‘An taɓa tofa min yawu a fuska saboda ni baƙa ce’

Mai sana’ar neman ‘yan ƙwallon kwando Sarah Chan ta zagaya faɗin duniya, daga Sudan zuwa Kenya, zuwa Turai da Amurka – amma sai da ta fuskanci yaƙi, da wariyar launin fata, da cin zarafi na jinsi kafin a kan hanyarta.

“An taɓa tofa min yawu a fuska kawai saboda ni baƙa ce,” a cewar tsohuwar ‘yar ƙwallon kwandon.

“Na fuskanci wariyar launin fata ta hanyoyi da yawa fiye da yadda nake tsammani.”

Yanzu, a matsayinta na mace ta farko da ke jagorantar tawagar neman ‘yan ƙwallo na gasar NBA – gasar ƙwallon kwando mafi girma a duniya – Ms Chan na ƙarfafa wa masu tasowa gwiwa don su yi amfani da damarmaki a ɓangaren wasanni.

Leave a Reply