An shawarci ma’aurata su yi koyi da Annabi SAW don dorewar Aurensu-Goro

Shugaban Kwamitin Ilimi mai zurfi na zauren majalisar wakilan kasar nan, Comrade Aminu Sulaiman Goro, ya shawarci Al’umma da su koyi da yadda Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wa sallam ya rayu da iyalan gidansa don samun dorewar aure a gidajen Ma’aurata.

Comrade Aminu Goro, ya bayar da wannan shawara ce a wajen taron Mauludin Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wa sallam, da kungiyoyin matasa Maza da Mata na tafiyar gidansa suka shirya.

Yace shi a kanki kansa ya zame masa wajibi ya yabawa mai dakinsa Hajiya Asma’u Aminu Goro, bisa yadda suka shafe shekaru 30 da aure ba tare wani a waje yaji kansu ba.

Kazalika Comerade Aminu Sulaiman Goro, ya bukaci ma’auratan wannan zamani da su cigaba da yin koyi da rayuwar magabata don samun albarkar Auren da zuri’a mai Yalwa, wacce Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi wa sallam, zaiyi Alfahari da ita a ranar Lahira.

Leave a Reply