An sanya sunan Mane cikin tawagar cin kofin duniya, duk da raunin da ya ji-Cisse

Mai horas da ‘yan wasan Senegal ya ce an sanya sunan Mane cikin tawagar kasar  da zasu fafata a Qatar, duk da raunin da ya ji.

Sunan Sadio Mane ya shiga cikin jerin ‘yan wasan da za su bugawa Senegal gasar Kofin Duniya da za a yi a Qatar duk da raunin da ya ji a ranar Talata.

An fitar da dan wasan mai shekara 30 daga fili a minti 45 na farkon wasan da Bayern Munich ta doke Weder Bremen da ci 6-1.

Gwarzuwar gasar Jamus din ta ce Mane ya ji rauni ne a “saman sangalalon kaurinsa na dama” kuma ba zai buga wasan da za ta yi ba da Schalke a ranar Asabar.

Senegal da ke rukunin A za ta fara wasanta da Netherland a ranar 21 ga watan Nuwamba.

kocin Senegal Alioy Cisse ya shaida wa taron manema labarai a Dakar babban birnin kasar a yau Juma’a.

Leave a Reply