An sanya Ronaldo a cikin tawagar Portugal da za ta gasar Euro 2024

Cristiano Ronaldo ya shirya  tsaf don fafatawa a babbaar gasar ƙasa-da ƙasa karo na 11, bayan da aka sanya sunansa a cikin jerin ƴan wasan tawagar ƙwallon kafar Portugal da za su waƙilci ƙasar a gasar cin kofin nahiyar Turai ta shekarar 2024, wato Euro 2024.
Ɗan wasan gaban na ƙungiyar A-Nassr mai shekaru 39, shine ɗan wasan da ya buga wa ƙasarsa wasanni fiye da kowanne ɗan wasa a tarihin ƙwallon ƙafa, inda ya yi wasa 206, ya kuma ci ƙwallaye 128.
Mai horar da Portugal, Roberto Martinez ya sanya Ronaldo a cikin ƴan wasan gaba guda 7 da ke cikin tawagarsa da za ta  fafata a gasar da za a yi wata mai zuwa a ƙasar Jamus.
A wani taron manema labarai, Martinez ya ce Ronaldo yana samar da aabin da ake buƙata a wajen cin ƙwallaye, kuma abin da ake buƙata kenan.
Ronaldo ya fara gasar Euro ne a shekarar 2004, lokacin da Portugal ta kai wasan ƙarshe, amma Greece ta lashe kofin.
Ɗan wasan da ya lashe kyautar Ballon d’Or har sau 5 ya taimakawa Portugal wajen lashe wannan kofi a shekarar 2016, da kuma Nations League a shekarar 2018-19.

Leave a Reply