An samu sabani tsakanin dillalan man fetur kan cire tallafi a Najeriya

Manyan kamfanonin dillalan man fetur da masu zaman kansu sun samu sabani kan batun cire tallafin mai da gwamnatin Najeriya ta ce za ta yi.

Yayin manyan dillalan suka shawarci gwamnatin kasar ta yi amfani da damar da aka samu ta raguwar farashin shigo da tataccen man daga waje ta cire tallafin, su kuwa dillalai masu zaman kansu sun ce yin haka ba tare da an gyara matutun kasar ba zai kara jefa ‘yan kasar cikin wahala.

Bangarorin biyu sun bayyana matsayinsu ne a kan batun tallafin man a wata tattaunawa da Jaridar The Nation a Abuja, bayan da gwamnatin kasar ta dora alhakin matsalar karancin man da ta ki ci ta ki cinyewa a kan ‘yan kasuwa da dillalai masu son cin kazamar riba.

A yayin tattaunawar ne Babban Sakataren kungiyar manyan kamfanonin dillancin man a Najeriya Clement Isong ya ce tun har a yanzu ana sayar da man a yawancin jihohi a kan naira 300 a kowa ce lita to kamata ya yi gwamnati ta yi amfani da wannan damar ta daina bayar da tallafin, wanda a yanzu ya kai naira tiriliyan 6.3

A ranar Talata ne shugaban kamfanin man fetur na Najeriya, NNPC, Mele Kyari y ace kudin shigo da man a yanzu ya ragu zuwa naira 295 kowa ce lita, inda ya kara da cewa ana kuma sayarwa ‘yan kasuwa a kan naira 113.

Leave a Reply