An samu raguwar masu kamuwa da HIV AIDS a Najeriya- NACA
Hukumar da ke yaki da cutar nan mai karya garkuwar jiki ta AIDS a Najeriya ta bayyana raguwar masu kamuwa da cutar HIV a sassan kasar nan idan an kwatanta da yadda kasar ke gani a shekarun baya.
Darakta Janar na hukumar Gambo Aliyu, da ya ke bayar da alkaluman cutar gaban taron manema labarai gabanin ranar yaki da cutar Sida ta duniya a ranar 1 ga watan Disamba, ya ce alkaluman masu kamuwa da cutar ya ragu daga mutum dubu 103 a shekarar 2019 zuwa mutum dubu 92 a shekarar 2021.
A cewar Gambo Aliyu, saukar alkaluman masu dauke da cutar ta HIV AIDS ka iya cimma kudirin Majalisar Dinkin Duniya game da rage masu kamuwa da cutar nan da shekarar 2030.
Gambo Aliyu ya ce daga watan Satumban da ya gabata akalla mutane miliyan 1 da dubu dari 619 ne ke karbar kulawar cutar ta HIV, lamarin da ke nuna karuwar masu samun kulawa idan an kwatanta da mutum dubu 838 wadanda ke karbar wannan kulawa a shekarar 2017.