An samu girgizar kasa a kudancin California……

An samu girgizar kasa a kudancin California wanda ya kasance mafi girma a tarihin kasar cikin shekaru 20.

Girgizar kasar mai sama da maki 6 ta afku ne a kusa da birnin Ridgecrest wanda yake da nisan kilometre 240 daga arewa maso gabas na birnin los Angeles.

Masu kashe gobara sun bada taimako wajan kashe wutar a ciki da wajen birnin.

Mutane daga dajin Mojave sun bayyana cewa sun ji karar girgizar kasar data afku a bikin zagayowar ranar yancin kai.