An sake dakatar da Sandro Tonali daga wasanni saboda karya dokar caca

Hukumar kwallon kafar Ingila ta dakatar da dan wasan Newcastle United, Sandro Tonali na watanni biyu, sakamakon karya dokar yin caca.

Dan kasar Italiya, mai shekaru 23, na cikin hukuncin dakatarwar wata 10 da aka yanke masa cikin Oktoban 2023, bayan da ya aikata laifin a Italiya, lokacin yana taka leda a AC Milan.

Cikin watan Maris hukumar kwallon kafar Ingila ta tuhumi dan wasan da cewar ya yi caca 40 zuwa 50 bayan da ya koma Newcastle daga AC Milan a watan Yuli, ciki har da yi a kan sakamakon wasannin kungiyar St James Park.

A watan Oktoban 2023 ma Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Italiya ta dakatar da ɗan wasan tsakiyar na tsawon wata goma saboda saɓa ka’idojin caca.

Leave a Reply